Shirin RAPID: An Sake Buɗe Shafin Cike Tallafin Shirin Ƙarfafa Tattalin Arzikin Yankunan Karkara a Najeriya

Shirin RAPID: An Sake Buɗe Shafin Cike Tallafin Shirin Ƙarfafa Tattalin Arzikin Yankunan Karkara a Najeriya

Shirin RAPID: An Sake Buɗe Shafin Cike Tallafin Shirin Ƙarfafa Tattalin Arzikin Yankunan Karkara a Najeriya

Rural Area Programme on Investment for Development (RAPID), wanda Bankin Masana’antu na Najeriya (BOI) ya ƙaddamar, na nufin ƙarfafa ci gaban tattalin arziki da rage zaman kashe wando a al’ummomin karkara da marasa karfi. Ta hanyar wannan shiri, ƙananan masana’antu da ’yan kasuwa za su samu tallafin kuɗi, shawarwarin kasuwanci da horo domin tabbatar da dorewar kasuwancinsu.

Manyan Manufofi:

  • Ƙarfafa ƴan kasuwa a yankunan karkara, musamman matasa da mata.

  • Samar da ayyukan yi ga matasa da mata.

  • Faɗaɗa harkokin tattalin arziki fiye da noma kaɗai a karkara.

Manyan Fasali:

  • Lokacin Biya: Har zuwa shekaru 3

  • Ribar Kuɗi: Kashi 5% a shekara

Sharuddan Cancanta:

  • Cikakken fom ɗin neman tallafi da tsarin kasuwanci.

  • Hujjar shaida (ID), BVN, NIN, da adireshin zama.

  • Cikakken fom na mai shaida (guarantor) da sauran sharuɗɗa.

Waɗanda Shirin Ya Shafa:

  • Ƙananan masana’antu da ’yan kasuwa.

  • Ƙungiyoyin al’umma a yankunan karkara.

Yadda Ake Nema: rapid.boi.ng/register

Karin Bayani: https://rapid.boi.ng/

Tuntuba: customercare@boi.ng | 0700-CALL-BOI (0700 225 5264)